A yayin taron kolin, jami’ai daga kasashen 2 zasu rattaba hannu a kan yarjejeniyoyin fahimtar juna da dama.
washington dc —
Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai bar Faransa a yau litinin zuwa birnin Cape Town, na Afrika ta Kudu, domin jagorantar karo na 11 na taron hadin gwiwar Najeriya da Afirka ta Kudu tare da takwaransa Cyril Ramaphosa.
Mashawarcin shugaba Tinubu a kan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a sanarwar daya fitar a jiya Lahadi, mai taken “Shugaba Tinubu zai jagoranci taron hadin gwiwar kasashe tare da takwaransa Shugaba Ramaphosa.”
A yayin taron kolin, jami’ai daga kasashen 2 zasu rattaba hannu a kan yarjejeniyoyin fahimtar juna da dama.
An kafa hukumar hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu a 1999 domin kara yaukaka zumunci da hadin kai tsakanin kasashen 2.