A gobe Laraba shugaban najeriya Bola Tinubu zai gabatar da kasafin kudin 2025 ga Majalisar Dokokin kasar.
Sakataren sashen bincike da yada labaran majalisar dokokin Najeriya, Dr. Ali Barde Umoru, ne ya bayyana hakan a harabar majalisar a Litinin data gabata.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake baiwa manema labarai tabbacin gabatar da kasafin kudin tare da neman jerin sunayen mutanen da za’a kyale su shiga zauren majalisar.
Makonni 3 da suka gabata, Tinubu ya aikewa zaurukan majalisun tarayyar 2, da matsakaicin kasafin kudin 2024-2026 inda aka kiyasta cewa za’a kashe Naira tiriliyan 26.1 a shekarar 2025.
Dandalin Mu Tattauna