A yau Alhamis, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya fara gudanar da ziyarar kwanaki 2 a kasar Faransa, inda dukkanin kasashen 2 ke neman karin alakar tattalin arziki sannan Paris ke neman yaukaka dangantaka da kasashen Afirka masu amfani da turancin Ingilishi sakamakon jerin koma bayan da ta samu tsakaninta da tsaffin kawayenta a nahiyar.
Macron ya tarbi takwaran nasa a ginin “Invalides Memorial Complex” na tunawa da tsaffin sojojin kasar mai dimbin tarihi, a abin da ke zama ziyarar aiki ta farko da wani shugaban Najeriya ya kai Faransa a fiye da shekaru 20.
Kammala taken kasashen 2 a farfajiyar daya daga cikin kasaitattun gine-ginen birnin Paris, ya kaddamar da ziyarar da za ta maida hankali wajen bunkasa alakar tattalin arziki tsakanin Faransa da Najeriya.
A yayin tarbar, shugaba Tinubu ya yi rangadin duba faretin ban girma.
Macron ya nemi ya sauya alakar Paris da Afirka tun bayan zabensa na 2017 da kuma bayan juye-juyen mulkin soja da sauyin dabi’u sun rage tasirin Faransa a nahiyar.
Ziyarar “dama ce da za ta kara yaukaka dadaddiyar alakar dake tsakanin Faransa da Najeriya”, a cewar ofishin Macron.
“Ina so in mika godiyata ga amini na, Shugaba Macron @emmanuelmacron, da wannan kyakkyawar tarba a wannan safiya yayin fara ziyarar aikina a Faransa,” kamar yadda Tinubu ya wallafa a shafinsa na X.
“Najeriya da Faransa na da tsohon tarihin alaka a fannoni da dama. Za mu fara tattaunawar diflomasiya domin gano sabbin fannonin da zamu kulla kawancen da zai amfani kasashenmu 2.”
Tinubu wanda ya isa Faransa a jiya Laraba ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnatin kasar.
Dandalin Mu Tattauna