A yau Laraba Fadar Shugaban Kasa ta sanar da tafiyar Shugaban Kasa Bola Tinubu ziyarar aiki a kasar Faransa.
Ziyarar za ta kasance mutuntawa ga gayyatar da Shugaba Emmanuel Macron ya yi.
Da yake bayyana hakan a cikin wata sanarwa, mashawarcin shugaban Najeriya na musamman a kan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, yace Macron da maidakinsa Brigitte za su tarbi Tinubu a gidan adana kayan tarihin sojojin Faransa "Les Invaides" mai shekaru 350 da kafuwa, da fadar shugaban kasar "Palaise L'Elysee domin bukukuwan farko da za su rikide zuwa tarurrukan diflomasiya."
"Ziyarar shugaban Najeriyar ta kwanaki 3 za ta maida hankali a kan karfafa dangantaka a fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma al'adu tare da samar da karin damammakin yin kawance musamman a bangarorin aikin gona da tsaro da ilimi da kiwon lafiya da bunkasa harkokin matasa da samar da guraben aikin yi da kirkire-kirkire da kuma sauya makamashi" a cewar sanarwar.
"Shugabannin 2 za su halarci tarurrukan siyasa da na diflomasiya da za su fayyace muradan bai dayan da kasashensu keda su a fannonin kudi da ma'adinai da cinikayya da zuba jari da kuma sadarwa.
Za kuma su halarci taron majalisar 'yan kasuwar Najeriya da Faransa, wacce ke kula da rawar da bangaren kamfanoni masu zaman kansu ke takawa a bunkasar tattalin arziki.
"Brigette da uwargidan shugaban Najeriya zasu tattauna akan burin da Remi Tinubu keda shi ta tallafawa mata da kananan yara da sauran marasa galihu ta hanyar shirin da ta kirkira na "sabunta fata".
Dandalin Mu Tattauna