Tinubu Na Ganawa Da Shugabanin Hadaddiyar Kungiyar Kwadago

Tinubu da Shugabanin Hadaddiyar Kungiyan Kwadago

Shugabanin hadaddiyar kungiyar kwadago na ganawa da Shugaba Bola Tinubu domin cigaba da tattaunawa akan mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya.

An hango Shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Joe Ajaero da takwararsa ta TUC, Festus Osifo suna shiga fadar shugaban kasa ta Aso Villa a yau Alhamis da rana.

Hakan na zuwa ne kimanin wata guda bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da cewa zai aikewa majalisar kasa kudiri akan mafi karancin albashi domin zartarwa.

Ana sa ran shugaban kasar ya yanke matsaya akan tayin Naira dubu 62 da bangaren gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu suka gabatar da kuma na Naira dubu 250 da bangaren ‘yan kwadagon ya gabatar.

Taron na zuwa kimanin wata guda bayan da Tinubu a jawabin daya gabatar a ranar dimokiradiya, 12 ga watan Yunin daya gabata, yace nan bada jimawa ba za’a aike da kudiri akan mafi karancin albashi daga bangaren zartarwa zuwa ga majalisar kasa domin a zartar da shi.

Ku Duba Wannan Ma Tinubu Zai Mikawa Majalisa Sabon Kudirin Mafi Karancin Albashi Nan Ba ​​Da Jimawa Ba