Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattaunawar Da Ake Yi Zata Samar Da Albashi Mafi Dacewa, Gwamnoni Sun Baiwa Ma’aikata Tabbaci


Kungiyar Gwamnonin Najeriya
Kungiyar Gwamnonin Najeriya

An ruwaito takardar bayan taron da kungiyar gwamnonin ta fitar na cewa, “gwamnonin sun amince su cigaba da tattaunawa da muhimman masu ruwa da tsaki domin samun matsayar da dukkanin bangarorin zasu amince da ita.”

Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewar za’a samu albashi mafi dacewa daga tattaunawar da ake yi tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da hadaddiyar kungiyar kwadago.

Gwamnonin sun bada tabbacin ne bayan wata ganawa da suka yi a jiya Laraba a Abuja.

An ruwaito takardar bayan taron da kungiyar gwamnonin ta fitar na cewa, “gwamnonin sun amince su cigaba da tattaunawa da muhimman masu ruwa da tsaki domin samun matsayar da dukkanin bangarorin zasu amince da ita.”

“Mun dukufa akan batun kuma muna bada tabbacin cewar za’a samu albashi mafi dacewa daga tattaunawar da ake cigaba da yi.”

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ne ya rattaba hannu akan takardar bayan taron.

Haka kuma, gwamnaonin sun tattauna akan wasu matsalolin dake addabar kasar nan, da suka hada da sauye-sauyen da ake cigaba da yi akan manufofin kudi dana haraji.

Ganawar gwamnonin na zuwa ne bayan da majalisar zartarwa ta tarayya ta jingine batun sake nazarin batun mafi karancin albashi domin cigaba da yin tuntuba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG