Tinubu Ba Zai Halarci Taron Kolin Majalisar Dinkin Duniya Ba

  • VOA Hausa

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

A cewar mataimaki na musamman ga shugaban a kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, Tinubu na so ya zauna a gida domin magance matsalolin dake addabar Najeriya.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron kolin Majalisar Dnkin Duniya karo (UNGA) na 79.

Sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar a yau Alhamis, tace Tinubu ba zai halarci taron kolin majalisar dinkin duniyar ba saboda yana so ya maida hankali a kan wasu batutuwa na cikin kasa.

A cewar mataimaki na musamman ga shugaban a kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, Tinubu na so ya zauna a gida domin magance matsalolin dake addabar Najeriya.

A sakon daya wallafa a shafin A, Dada Olusegun ya rubuta cewa “shugaban kasa ba zai halarci taron kolin Majalisar Dinkin Duniya na bana ba saboda bayan balaguron da yayi zuwa kasashen China da Burtaniya, yana so ya mayar da hankali akan wasu batutuwa na cikin gida tare da warware wasu daga cikin matsalolin dake addabar kasar, musamman bayan mummunar ambaliyar ruwan data afku a baya-bayan nan.”