Texas-Dussar Kankara Ta Haifar Da Dauke Wuta A Gabashin Amurka

Dussar Kankara a Texas

Wani hadarin tarihi na lokacin sanyi da ya kara tsananin sanyi a akalla rabin fadin Amurka, ya sa sama da mutum miliyan biyu da rabi a Texas sun rasa wutar lantarki.

An ci gaba da samun dussar kankara da tsananin sanyi dab a a saba gani ba a yau Laraba a kudu maso yammacin Amurka inda hasashe ya nuna sanyi zai dada karuwa. Yanayin sanyin da ba a saba gani a yankin ba, yasa bukatar wutar lantarki ta karu, lamarin da ya yi sanadiyar kamfanin wuta mai zaman kansa dake aiki a jihar ya gaza biyan bukatar jama’a kana kayan aikin kamfani suka samu matsaloli.

A wata tattaunawa, alkaliyar lardin Harris, Lina Hidalgo, da lardinta ke cikin birnin Houston, ta ce wasu dauke wutar sun zo ne kai tsaye sakamakon yanayin, amma kuma an gyara matsalolin da dama.

Masu amfani da wutar da gidajen su ba wuta, suna shiga layukan sayin abinci da kayan marmari a tashoshin sayar da fetur a Pflugerville, a Texas, a jiya 16 ga watan Faburairu shekarar 2021.

Amma ta ce galibin matsalolin da jihar ke fama da ita, bala’i ne na dan Adam, kama daga yanda ake tafiyar da bada wutar lantarki da kamfanin Electric Reliability Council of Texas (ERCOT) ke yi. Ta ce mazauna yankin baki daya sun cancanci a basu amsoshi.

Shugaban kamfanin wutar na ERCOT Bill Magness, ya ce kamfanin ya yi kokarin shiryawa hadari, amma yayin da yanayin ke kara muni a ranakun Litinin da Talata, sai na’urori suka daina aiki. Wasu ‘yan siyasa a jihar mai yawan man fetur da iskar gas, suna dora laifi a kan tsarin samar da wuta daga halitta, suna fadin cewa na’urar buga iska da ta daskare kankara ce ta haifar da wannan matsala.

Magness ya ce sanyi ya kama na’urar kada iskar amma kuma ya ce wuta mai yawa dage iskar gas da gawayin coal sun dauke. Ya ce kokarin magance dauke wutar shine hanya daya tilo na dakile mummunar daukewar wuta a Texas.

Ya zuwa yau Laraba, Magness ya ce ERCOT ba zata iya bada takamaiman tsari kan lokacin maido da wutar cikakke. Gwamnan Texas dan Republican Greg Abbort, ya yi kira ga gudanar da bincike a kan hukumar.

An yi hasashen ci gaba da samun tsananin sanyi zuwa akalla ‘yan kwanaki masu zuwa a Texas da waurare da dama rabin gabashin Amurka.