Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Majalisar Dattawan Amurka Ta Wanke Trump


Zaman da Majalisar Dattawa ta wanke Trump ranar Asabar, ranar 13 ga watan Fabrariru, 2021. (Senate Television via…
Zaman da Majalisar Dattawa ta wanke Trump ranar Asabar, ranar 13 ga watan Fabrariru, 2021. (Senate Television via…

Majalisar Dattawan Amurka, ta wanke Donald Trump a yunkurin tsige shi da aka yi a karo na biyu cikin shekara guda, inda ‘yan Republican suka hana a dora masa laifi mummunan harin da magoya bayansa suka kai a ginin majalisar dokokin kasar.

Sanatoci 57 ne suka amince a dora laifin akan Trump, yayin da 43 suka nuna akasin hakan, yunkurin da ya gaza samar da biyu cikin kashi uku na rinjayen da ake bukata kafin a tsige shugaban kasa.

An tuhumi Trump ne da laifin cewa shi ya tunzura magoya bayansa suka mamaye ginin majalisar a ranar 6 ga watan Janairu, jim kadan bayan wani jawabi da ya gabatar.

An dai kwashe kwana biyar ne ana zaman sauraren muhawarar a zauren majalisar.

A Wannan kada kuri’a da majalisar ta yi a ranar Asabar, bakwai daga cikin ‘yan Republican 50 ne suka marawa ‘yan Democrat baya domin ganin an tsige Trump.

Bayan da aka wanke shi, Trump ya fada cikin wata sanarwa cewa, “wannan wani babi ne bi-ta-da-kullin siyasa mafi girma a tarihin kasarmu. Babu wani shugaban kasa da ya taba fuskantar wani abu makamancin wannan.”

A nashi bangaren, shugaba Joe Biden cikin wata sanarwa ya ce, “duk da cewa kada kuri’ar da aka yi a karshe bai kai ga an same shi da laifi ba, dalilin da ya sa aka tuhume shi bai sauya ba.”

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG