Tawagar Pentagon a karkashin jagorancin Mataimakin Sakataren Tsaron Amurka mai kula da Aiyuka na Musamman, Christopher Maier da Darektan Sashen Kula da ci gaban Rundunonin Mayaka a Ma’aikatar Tsaron Amurka, Janar Dagwin Anderson, ta iso Nijar yayin da ake a ci gaba da yunkurin zakulo hanyoyin kwashe dakarun Amurkar daga kasar.
Jami’an biyu na tafe ne dauke da daftarin fasalin wadannan aiyuka.
Sun gana da Ministan Tsaro, Janar Salifou Mody a yammacin Laraba 15 ga watan Mayun 2024 a matsayin share fage, koda yake kuma bangarorin ba su yi wata sanarwa ba a karshen ganawar.
Duk da haka, masana akan harkokin tsaro sun fara tofa albarkacin bakinsu kan lamarin inda Moustapha Abdoulaye, kwararre akan harkokin tsaro da huldar kasa da kasa yace “taron zai sa kasashen biyu su ciyo kan wannan matsala kuma cikin daraja ba sai an yi wannan hayaniya ba wadda kasar Faransa ta sha a watan Satumba da ya wuce.
Ya kara da cewa "ko Sojojin Amurka sun janye daga Nijar ina tsammanin za su samu yarjejeniya ta yanda watakila sojojin na Nijar za su kara samun horo daga wajen Amurka…..”
Shima Dr Abba Seidick masani ne akan sha’anin tsaro a yankin Sahel, kuma yace “Amurka babbar kasa ce tana karfi tana kuma da abubuwa da yawa ina tsammanin sojojin da suke mulki a Nijar basa son wani cikas ya shiga tsakanin su da Amurka. Saboda da haka wannan tawaga ta zo zata yi dan kwanaki a nan Nijar ta bada shawara ga sojojin Nijar kuma su ga yanda ake yi”. a cewarsa
An dai bayyana cewa wannan tawaga za ta tattauna da kwararrun sojojin Nijar a kan daftarin da ta zo da shi don ganin aiyukan kwashe sojojin Amurka sun gudana cikin tsari da tsaro a wa’adin da ya dace.
A ranar 15 ga watan Maris 2024 ne hukumomin mulkin sojan Nijar suka bada sanarwar yanke huldar aiyukan soja da Amurka, sakamakon abinda suka kira rashin halaccin yarjejeniyar da kasashen suka cimma a 2012, matakin da ke nuna bukatar ficewar dakaru 1100 da Amurkar ta girke a arewacin wannan kasar.
Rashin gamsuwa da yanayin da ake ciki a fagen daga shekaru fiye da 10 na yaki da ta’addanci ya sa sojojin Nijar kifar da gwamnati a ranar 26 ga watan Yulin 2023 lamarin da ya sa hukumomin mulkin sojan aiwatar da canje-canje, ciki har da korar sojojin da wasu kasashen yammaci suka girke farawa da wacce ta yi wa Nijar mulkin mallaka wato Faransa mai sojojin da aka kyasta cewa yawansu ya doshi 5000 a yayin da Rasha ta fara aiko da dakaru da aka ayyana a matsayin masu aikin horo.
Ga sautin rahoton wakilin Muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5