Tawagar Amina Mohammed da ta samu rakiyar ministan harkokin wajen Sweden da shugabar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) sun gana da sarakunan gargajiya da shugabannin addinai da kuma kungiyoyin mata.
Haka kuma tawagar ta ziyarci fadar shugaban kasa inda suka gana da shugaba Muhammadu Isuhu.
A cewar Aisha Mohammed, ta kai wannan ziyara ne domin tattaunawa da shugaban kasa da masu ruwa da tsaki kan harkokin mata, da kuma baiwa mata damar taka rawa a fanoni daban-daban.
MDD na kokarin taimakawa wajen wayar da kai ga gwamnatoci kan kula da matsalolin mata da suka hada da yin auren wuri da kuma baiwa mata damar rike mukaman gwamnati da shiga harkokin siyasa.
Tawagar Amina dai ta je karkarar Maradi, domin ganewa idanunta zahirin halin da mata ke ciki, a wani yunkurin tantance mizanin ayyukan da kungiyoyin da ke samun tallafin MDD ke gudanarwa akan maganar inganta rayuwar mata.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Your browser doesn’t support HTML5