Tawagar kungiyar tarayyar Afirka na Burundi da zummar kawo shirin zaman lafiya

Wasu shugabannin Afrida: Shugaban Somalia a hagu na Najeriya a tsakiya da na Kenya a dama

A yau Juma’a wata tawagar wakilan kungiyar tarayyar kasashen Afrika na ci gaba da ziyara a kasar Burundi domin ganin ta hada kan bangarorin da ke rikici a kasar, saboda a shawo kan takaddamar siyasar kasar.

Ziyarar na guda ne a karkashin jagorancin shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma, wanda ake sa ran zai gana da bangaren gwamnati da na ‘yan adawa da kuma shugabannin kungiyoyin fararen hula.

Wannan ziyara na zuwa ne bayan wacce babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya kai kasar a wannan mako, shima a wani yunkuri na shawo kan rikicin kasar da aka kwashe watannin goma ana yi.

Shugaban wani shirin kare aukuwar rikic-rikice a yankin tsakiyar Afrika, Richard Moncrieff, ya ce, ya yi kira ga tawagar wakilan ta AU, da su gayawa bangarorin da ke rikici a kasar ta Burundi cewa za a dauki tsauraran matakai akansu, muddin ba su ba da hadin kai ba, tare da kiran a gudanar da wani zama a wajen kasar ta Burundi.

Mr. Moncrieff ya kuma zargi gwamnatin ta Burundi da muzgunawa masu adawa da ita, tare da baiwa mambobin mayakan sa kai manyan mukaman tsaro.