Jakadun kasashen ne suka bayyana haka lokacin da suka kaiwaministan kasashen ketare na kasar Kamaru Jean Mbela Mbela takardun a ofishinsa dake birnin Yawunde, domin mikawa shugaban kasar. Sun dai bayyana irin yunkurin da gwamnatocin kasashensu ke yi na marawa kasar Kamaru baya a yaki da ta’addanci.
A cikin jawabinta jakadiyar kasar Faransa a kamaru Christine Robynson tace kasarta zata yi kokari gaya wajen taimakawa kasar Kamaru da dakarun tsaro, da kayayyakin yaki irin na zamani, da kuma bayarda labaru na sirri, kan yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.
Ta bayyana cewa, akwai yarjejeniya tsakanin kasar Faransa da kuma Kamaru na taimakawa da kayan yaki, musamman a duk lokacin da kasar ta Kamaru ta shiga yaki da wata kasa, ko irin yadda yanzu haka kasar take fama da mayakan Boko Haram.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Garba Lawal ya aiko da kasar Kamaru