Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rwanda Za Ta Kwashe 'Yan gudun Hijrar Burundi


Burundi's President Pierre Nkurunziza tare da Jakadiyar Amurka Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power yayin wata ziyara da ta kai a kasar
Burundi's President Pierre Nkurunziza tare da Jakadiyar Amurka Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power yayin wata ziyara da ta kai a kasar

Gwamnatin Rwanda ta ce za ta kwashe ‘yan gudun hijrar da suka fito daga Burundi zuwa wasu kasashe, bayan zargin da wani jami’in diplomasiyyan Amurka ya yi cewa Rwanda ta na horar da ‘yan tawayen da ke adawa da gwamnatin Burundi.

Hukumomin Rwanda sun fitar da wannan sanarwa ce a jiya Juma’a, inda suka ce za su hada kai da sauran kasashen waje domin sauyawa ‘yan gudun hijrar matsuguni.

Wannan sanarwa ta zo wa Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya da mamaki, inda ta nuna damuwarta kan yadda kasar ta Rwanda ke shirin datse ayyukan lura da ‘yan gudun hijra da ta kwashe shekaru da dama ta na yi.

Burundi ta jima tana zargin Rwanda da marawa ‘yan tawayen kasar ta baya, wadanda ta zarga da cewa suna shirin kifar da gwamnatin da ke Bujumbura, babban birnin kasar, zargin da itama Rwandan ta sha musantawa.

Rikicin Burundi ya samo asali tun bayan da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya ayyana shirinsa na tsayawa takarar neman shugabancin kasar a watan Aprilun da ya gabata, lamarin da ‘yan adawa suka ce ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Tuni dai shugaba Nkurunziza ya lashe zaben da aka yi a bara.

XS
SM
MD
LG