Tawagar Hamas Na Shirin Kai Ziyara A Misra Don Ci Gaba Da Tattaunawar Tsagaita Wuta A Gaza

  • VOA Hausa

Lebanon Israel Palestinians

Nan bada dadewa ba tawagar Kungiyar Hamas ta Falasdinawa zata isa kasar Misra domin shiga tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza, a cewar wata sanarwar da kungiyar ta fitar yau Alhamis.

Sanarwar ta kara da cewa, yayin wata hirar waya da shugaban hukumar liken asirin Misra Abbas Kamel, shugaban Hamas Ismail Haniyeh ya jaddada matsayar kungiyar ta yiwuwar amincewa da shirin tsagaita wuta bayan nazarin shawarwari.

Israel Palestinians

A ranar Asabar ne Hamas ta ce ta samu matsayar Isra’ila ta baya bayan nan, amma zata yi nazari akai kafin ta bada martani.

Kamfanin dillancin labaran Misran na Al-Qahera ya ambato wata babbar majiyar Misra da ba a iya tantancewa ba tana mai cewa tawagar kungiyar Hamas zata iso Alkhira cikin kwanaki biyu masu zuwa.

Da yake magana da Reuters, wani jami’in Falasdinu mai kusanci da masu shiga tsakanin ya ce ziyarar tawagar Hamas zata iya kasancewa kwanaki biyu masu zuwa.

Israel Palestinians

Sanarwar Hamas ta kara da cewa manufar tattaunawar ta birnin Alkahira, itace cimma yarjejeniya mai ma’ana da mutanen mu ke bukata da kuma zata kawo karshen zalunci.