Tawagar Najeriya Zata Gana Da Hukumomin Jami’ar Burtaniya Akan Umarnin Dawo Da Dalibai Gida

Shugabar Hukumar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa

Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya Mazauna Ketare (NIDCOM) ce ta bayyana hakan a cikin sanarwar data fitar a jiya Laraba.

Wata tawagar gwamnatin tarayyar Najeriya zata gana da jami’an jami’ar “Teesside” dake Burtaniya domin warware takaddamar zargin bada umarnin dawo da wasu daliban Najeriya ba bisa ka’ida ba a yayin da suke tsaka da karatu a makarantar.

Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya Mazauna Ketare (NIDCOM) ce ta bayyana hakan a cikin sanarwar data fitar a jiya Laraba.

A ranar 22 ga watan Mayun da muke ban kwana da shi, wasu daliban Najeriya suka gudanar da wata zanga-zanga sakamakon umarnin da hukumomin jami’ar suka bayar na cewar su bar Burtaniya bisa zargin wasunsu da gaza biyan kudaden makaranta.

Daga bisani Shugabar Hukumar ta NIDCOM ta gana da wasu daga cikin daliban ta na’ura a Lahadin data gabata inda aka amince cewar wakilai daga ofishin jakadancin Najeriya dake Burtaniya, inda Jakada Christian Okeke zai jagoranci wata tawaga domin ganawa da hukumomin gudanarwar jami’ar da nufin warware takaddamar.

Shugabar Hukumar ta NIDCOM ta kuma bukaci daliban su kwantar da hankulansu tare da kaucewa daukar doka a hannunsu inda ta roki hukumomin jami’ar dasu mutunta su.