Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Yi Jigilar Karshe A Aikin Kwaso ‘Yan Kasar Daga Sudan


Tawagar 'yan Najeriya ta karshe da aka kwaso daga Sudan (Hoto: Twitter/NIDCOM)
Tawagar 'yan Najeriya ta karshe da aka kwaso daga Sudan (Hoto: Twitter/NIDCOM)

“Babu ran dan Najeriya ko daya da ya salwanta izuwa yanzu,” a cewar hukumomin kasar.

Hukumar da ke kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare NIDCOM, ta ce an kammala jigilar kwaso ‘yan kasar da suka makale a Sudan da ke fama da rikici.

A ranar 15 ga watan Afrilu fada ya barke tsakanin sojoji da dakaru na musamman (RSF.)

Daruruwan mutane sun mutu yayin da dubbai suka jikkata.

Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta ce dubban daruruwan mutane sun fice daga muhallansu.

“A ranar Asabar 13 ga watan Mayu, jirgin Tarco Air ya sauka a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe da misalin karfe 8:30 na dare a Abuja, dauke da mutum 147.” Hukumar ta NIDCOM ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Asabar.

Sanarwar ta kara da cewa na kwaso fasinjojin karshen ne daga filin tashin jirage na kasa da kasa da ke Port Sudan.

Wannan zangon fasinjoji na karshe shi ne na 15, wanda hakan ya kai jimullar mutanen da “gwamnatin tarayya” ta kwaso zuwa 2,518 a cewar NIDCOM.

“Babu ran dan Najeriya ko daya da ya salwanta ya zuwa yanzu,” a Sudan a cewar hukumomin Najeriya.

XS
SM
MD
LG