ABUJA, NIGERIA - IMF ya kara da cewa matsalar tsaro da kuma koma-baya da harkar noma ya tsinci kansa a kasar ya kara tsunduma ‘yan kasar cikin matsin rayuwa.
IMF ya ce karancin kudin shiga, rashin tabbas game da kayan masarufi da kuma talauci su na daga cikin abinda ya ta'azzara tsadar rayuwa a kasar. Don haka ya kamata hukumomi su mayar da hankali wajen samar da hanyoyin da zasu tallafa domin bunkasar tattalin arziki.
Rahoton ya ce janye tallafin man-fetur, faduwar darajar Naira da kuma koma-baya a fannin noma, sun taimaka wajen tsadar rayuwa a kasar, IMF ta kara da cewa karancin biyan haraji shima na daga cikin abinda ke kawo tsaiko wajen aiwatar da ayyuka domin ci gaban al'umma.
IMF ya ce Najeriya na fuskantar karancin tallafin kudi daga kasashen ketare, fama da kalubalen cikin gida da kuma tsadar rayuwa sakamakon tashin farashin kaya da ya shafi duniya.
Kazalika, IMF ya ce duk da haka, yanzu Najeriya na da kudaden da zata iya fara biyan bashin da ta ke bin ta.
‘Yan Najeriya na kara bayyana yadda tsadar rayuwa ke shafar su da kuma yadda hauhawar farashin kaya ke zamo musu wani babban kalubale.
A hirarsa da Muryar Amurka, Yusha'u Aliyu masani kuma me sharhi kan lamuran da suka shafi tattalin arziki ya ce "rahoton IMF ba abin mamaki ba ne, ganin cewa yadda yanzu lamura ke tafiya a kasar game da tsadar rayuwa, wanda yawan bashi da ake bin kasar da kuma kalubalen tsaro da kasar ke fama da shi, sun kawo wa kasar koma-baya a fannin tattalin arziki.
Aliyu ya kara da cewa "dole ne IMF ta bi bayan kudaden lamunin da suka baiwa Najeriya domin aiwatar da ayyukan ci gaba, rashin yin hakan yana daga cikin abinda ke kara tabarbarar da tattalin arzikin kasar"
Yanzu dai hankulan yan kasar ya karkata ne ga gwamnatin tarayya domin ganin matakan da za ta fito dasu domin ceto su game da halin tsadar rayuwa.
Saurari cikakken rahoto daga Rukaiya Basha:
Your browser doesn’t support HTML5