Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata Gwamnatin Ghana Ta Sake Duba Manufofinta Na Haraji A Kasafin Kudin 2024 – Hadakar Kungiyoyin Kwadago


Gwamnatin Ghana Ta Yi Duba Ga Manufofinta Na Haraji A Kasafin Kudin 2024 – Hadakar Kungiyoyin Kwadago
Gwamnatin Ghana Ta Yi Duba Ga Manufofinta Na Haraji A Kasafin Kudin 2024 – Hadakar Kungiyoyin Kwadago

Hadakar kungiyoyin kwadagon Ghana (GFL) ta yi kira da babbar murya ga gwamnati da ta gaggauta sake duba manufofinta na haraji. Hadakar ta jaddada cewa idan an yi garambawul ga manufofin haraji, hakan zai iya samar da ingantaccen yanayin kasuwanci da kuma inganta yanayin rayuwa ga dukkan 'yan Ghana.

A cikin wata sanarwa da ta tura wa manema labarai, mai dauke da sa hannun babban sakatare Abraham Koomson, hadakar ta yi ikirarin cewa harajin da ake cewa ‘Nuisance Taxes’ a turance, wato wani kaso na farashin sayar da kaya ko ayyuka, wanda mai sayen kaya ke biya kuma mai siyarwa ya aika zuwa ga hukumar haraji na kasa, na haifar da koma bayan ci gaban tattalin arziki ta hanyar dakile ci gaban kasuwanci tare da dorawa ‘yan kasa wahalhalun tsadar rayuwa, da kuma kawo cikas ga ayyukan masana'antu.

Hadakar kungiyar ta GFL ta ce ta yi imanin sake duba harajin na ‘nuisance taxes,’ da na wasu kayayyaki da aka ambata abu ne da ke bukatar matakin gaggawa." Domin haka, gwamnati ta ba da fifiko wajen duba hakan a kasafin kudin 2024.

Wani bincike na baya-baya da hadin gwiwar kamfanin KPMG da hukumar UNDP suka gudanar, ya bayyana matukar tasirin da haraji kan harkokin kasuwanci ke yi, a yayin da ake shirye-shiryen gabatar da kasafin kudin shekarar 2024.

Harajin da binciken ya gano, da ke bukatar a yi duba a kansu, sun haɗa da harajin sakon kudi na elektronik (E-Levy), harajin COVID-19, harajin shigowa da kaya, harajin man fetur, da harajin ci gaba mai dorewa. Wadannan harajin na ci wa ‘yan kasuwa tuwo a kwarya, wanda ke janyo tsadar kayayyakin masarufi ga ‘yan kasa.

Hamza Attijjani, mai sharhi kan tattalin arziki da harkokin kudi, yace lallai “Haraji na cikin hanyoyin da gwamnati ke samun kudaden gina kasa, sai dai wani lokacin haraji na shafar kasuwanci idan ba a bi hanyoyin da suka dace ba.”

Yace, Ghana na samun kashi 13 cikin 100 na haraji a kudaden da take samu na shiga. A saboda haka, daga cikin yarjejeniyarta da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) wanda ya gindaya cewa, “kowane wata hudu ya kamata Ghana ta kara haraji; wato idan ba a kirkiro sabbin haraji ba, to a kara kan wadanda ake da su.”

Attijjany ya shawarci gwamnati da ta janye harajin da ke da mafi karancin tasiri ga bukatunsu domin ya rage radadi ga kasuwanci da jama’ar Ghana.

Yawan harajin da gwamnati ta sanya wa kayayyaki da wasu ayyuka na matukar tasiri ga rayuwar jama’a wajen biyan bukatun yau da kullun da kuma tallafa wa iyalansu.

Osuman Yusha, ma’aikacin banki ne, ya bayyana ra’ayinsa a kan batun.

Ba zan ce a fidda haraji ba sam, amma a duba a rage ko kuma a dorawa wasu bangaren mutane da za su iya biya ba da wahala ba, domin kasa na ci gaba ne da haraji da take samu daga al’ummarta”.

Nan take dai ma’aikatar kudi bata ce komai ba game da kiran da hadakar kwadagon ta yi.

Saurari rahoton Idris Abdullah:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:31 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG