Shugabar Asusun Lamuni na Duniya (IMF) Kristalina Georgieva ta taya Ghana murnar samun rancen da ta bukata daga IMF.
“Ina taya Ghana murnar gagarumin shirin sauye-sauyen farfado da ci gaba da kuma rage yawan basussukan da ake bin kasar da ta ke yi. Na kuma yi farin ciki kan yadda hukumar zartarwar IMF ta amince da shirin tallafin dala biliyan 3 na tsawon shekaru uku. Muna alfahari da kasancewa abokan hadin gwiwa da Ghana wajen magance matsalar kudi da kasar ke fuskanta,” a cewar Kristalina.
A wani taron manema labarai na hadin a birnin Washington DC da gwamnatin Ghana da jami’an IMF suka shirya ta kafar Zoom, Ministan Kudin Ghana Ken Ofori-Atta ya bayyana tsarin tallafin kudin na IMF nan da watanni masu zuwa. Yace, za a ba da dala miliyan 600 ranar Juma'a, sai kuma dala miliyan 600 bayan watanni 6.
Ana sa ran samun kashi na biyu na dala miliyan 600 a cikin watan Nuwamban 2023, sannan ragowar kudin za a kasa su kan dala miliyan 360 a duk wata shida, idan har kasar ta cika sharuddan shirin na IMF.
Nuhu Eliasu, malamin tattalin arziki da harkokin kudi a jami’ar Islamiya ta Ghana, a wata hira da Muryar Amurka ya bayyana dalilin da ya sa asusun IMF ya kasa kudaden maimakon ba da jimlar kudin.
Yace, idan Ghana ta iya cika sharuddan da hukumar ta gindaya mata, to za a bata kashin kudaden nan gaba. Kuma haka tsarin zai kasance har a kammala ba da kudaden.
Sai dai masana tattalin arziki kamar Hamza Adam Attijjany, na nuni da cewa, lokacin da talaka zai samu amfanin wannan tallafin bai kai ba tukunna, domin sharuddan da IMF ta gindaya na kara haraji da dauke wasu tallafi ga jama’a za su iya kara matsin rayuwa ga jama’a cikin dan lokaci.
Ya kara da cewa, amma idan gwamnati ta cika alkawarin ba da tallafi ga manoma, to za a iya samun saukin kayan abinci da wasu kayan masarufi, sannan za a samu karin masu zuba hannun jari a kasar.
Matsin tattalin arziki mafi muni da aka gani cikin shekaru da dama ne ya tilasta wa shugaba Nana Akufo-Addo sauya ra’ayinsa komawa ga asusun IMF.
Saurari rahoton Idris Abdallah: