Ga mafi yawan ‘yan Afrika mazauna Amurka, damar kada kuri’a, dama ce ta nuna tasirinsu a harkokin siyasar kasar da kuma bada gudummuwarsu ga al’umma.
Ivo Tasong, dan kasar Kamaru da ya kaura zuwa Amurka a shekarar 1986, yace kada kuri’a ba abu ne da zai yi wasa da shi ba.
Ya ce“Yadda na samu sa’ar kaura na zauna a nan Amurka, ba zan dauki ‘yancin damar kada kuri’a da wasa ba, saboda mun san halin da iyalanmu ke ciki a can gida,” Muna cikin yaki yanzu haka inda muka rasa da yawa daga cikin iyalanmu da abokanmu. Kuma kokarin gwamnati ya gaza wajen kira a samu zaman lafiya da sasantawa cikin lumana. Kuma nan idan muka yi wasa da damarmu to sai ya kasance mun yi biyu babu.”
Tasong na daya daga cikin mutane miliyan 2.4 da aka kiyasta a matsayin “yan Afrika da aka Haifa a waje dake zaune a Amurka, wadanda mafiya yawansu suna da damar zabe, bisa ga wata kididdiga kidaya a nan Amurka.
Tasong yana kasuwanci a fannin fasaha a birnin Silver Spring dake jihar Maryland, kuma shine shugaban wata kungiyar siyasar ‘yan asalin kasar Kamaru da ake kira U.S-Cameroon Democracy Network, wata kungiya dake kula da Amurkawa ‘yan asalin kasar Kamaru.
Duk da cewa yana goyon bayan Joe Biden, dan takarar shugaban kasa na jam’iyar Dimokrat, ya kuduri aniyyar yiwa mutane masu bambancin ra’ayin jamiyyu daban daban ragista domin su kada kuri’a a zaben na Talata uku ga watan Nuwamba.
Yace, “Abinda muke kokarin yi shine mu nunawa dukkan al’ummarmu cewa, ba yadda zamu zauna mu ci moriyar wuri kuma mu ki shiga zabe, saboda duk abinda ke da muhimmanci ga Amurkawa na asali muma yana da muhimmanci gare mu a matsayinmu na al’umma.” Ku fita ku kada kuri’unku da sanyin Safiya. Idan ana ruwa, ku dauki lema. Ku kasance a wurin.
Ba Tasong ba ne kadai mai irin wannan sha’awar.
Wani rahoto da cibiyar bincike da ake kira "Pew Research Center" ta gudanar ya bayyana cewa, masu kada kuri’a bakaken fata sun fi kowa jajircewa a zaben na 2020. Cibibiyar Pew ta kuma gano cewa, baki bakaken fata na bada kuri’u a dungule. Tsakanin shekarar 2020 da 2018 an samu karuwar adadin masu zabe baki bakaken fata daga dubu 800,000 zuwa miliyan 2.3.
Mukaddashin darekta a cibiyar Pew Neil Ruiz ya bayyana cewa, “Mun ga karuwar masu kada kuri’a ninki biyar na baki bakaken fata” Yace masu kada kuri’a ‘yan asalin Afrika zasu ci gaba da yin tasiri kasancewa cibiyar Pew ta gano cewa, masu kada kuri’a ‘yan asalin Afrika zasu ci gaba da taka muhimmiyar rawa sabili da sun fi karancin shekaru akan ragowar mafiya yawan masu kada kuri’an
Duk da cewa kuri’ar jin ra’ayin jama’a na nuna da dama daga cikin masu kada kuri’a bakaken fata suna goyon bayan Biden ne a zaben shugaban kasa, ‘yan Afrika mazauna kasar waje ba zaben mutum daya suke ba a kungiyance. Babu kuma wani bincike da ya nuna jam’iyar da su ke goyon baya .
Wadansu daga cikin al’ummar ‘yan Somaliya dake Minneapolis, sun bayyana cewa, jam’iyar Republican za su zaba. Daya daga cikin mutanen, Sahra Yassin Farah tace ta shiga damuwa bayan da ta yi shekaru tana zabar Democrats. Ta ce tana so ta ga ana jaddada shirye shirye don matasa dake cikin hadari da kuma farfado da tattalin arziki.
Ta shaidawa Sashen Somaliya na Muryar Amurka cewa, “idan na ga yara basu da wani tsari, basu da cibiya a unguwanninsu da za ta taimaka wa yara. Muna da matsaloli da yawa da yara na shaye shayen kwayoyin. Muna da yara da yawa da suka shiga kurkuku. An haifesu ne a cikin shekaru ashirin da na ke nan. Idan na dubi tsare tsaren Democrat, al’amura ba za su sauya ba”
Wasu “yan Afrika mazauna kasashen ketare sun bayyana bukatar a kula da na kasa tukun ba tare da nuna banbancin jam’iyya ba.
Wata mace da Muryar Amurka ta yi hira da ita mai suna Olanike “Nike” Adebayo wadda ta girma a Chicago kuma ‘tana da tushe a Najeriya ta bangaren mahaifiyarta. Ta bayyana cewa ta zauna a Miami a gundumar Dade Florida inda ta ke aikin Lauya mai kare iyali da kuma wadanda ake tuhuma da aikata manyan laifuka. Ta kuma tsaya takarar neman kujerar Alkali a shekarar 2018 da kuma watan Agusta. Sai dai bata samu nasara ba a lokuta biyun amma ta ce ta kuduri aniyar ci gaba da kutsa kai a takarar nan gaba.
Yayinda zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu su ke daukan hankali a duk fadin kasar Adebayo tace tsayawa takara a wasu zabukan suna da muhimmanci.
Abdulaziz Osman ya bada gudummuwa a rubuta wannan rahoton