Tashin Farashin Kaya Lokacin Azumi

Musulmai a Najeriya da ma wasu sassa a duniya suna azumi a wannan wata mai tsarki na Ramadan da kama baki daga daren assubahi zuwa magariba.

Azumi ya zo maimakon farshin kaya yayi kasa sai tashin goron zabi yayi lamarin da ya sa mutane da mutane ke kuka dashi.

Shugaban 'yan kasuwan Najeriya ya bada wasu hujjoji da suka kawo tashin farashin kaya lokacin azumi.

Yace tshin farashi ba'yan kasuwa ba ne suka jawo hakan. Yace lamarin ya faru n saboda dalilai daban daban. Misali karancin doya da dankali ya sa an samu karin farashinsu. 'Yankasuwa ba manoma ba ne. Masu noma daban 'yan kasuwa kuma daban suke.

Matsalar rashin samun damina da wuri kamar yadda aka saba ya sa sabon dankali bai shigo ba. Saboda haka an samu tashin farashi domin tsohon ya kare.

Kasuwar hatsi a Najeriya

Dankali kadan da ya saura a hannun manoma ya sa sun kara mashi kudi. Haka ma doya. Shinkafa kuma nada nata daban. Rufe iyakokin kasar da aka yi ya kawo karancin shinkafa. Abu na biye da wannan shi ne dalar da ake canzawa a sayo kaya ita ma ta haura.Kowa ya san yadda farashin dala ya tashi a kasar.

Shugaban yace suna kokarin su gayawa manyan kamfanoni da hukumomin da abun ya shafa su nemi hanyar kawo sassauci saboda jama'a su samu sauki.

Ana rokon hukumomi su rage harajin da suke karba akan kaya su kuma rage matsin da suke yi. Su tabbatar an samu man mota wadataccedomin kudin sufuri ya sauko.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Tashin Farashin Kaya Lokacin Azumi