Alhaji Grema Terab shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno shi ya battabar cewa Amurka ta baiwa Najeriya tallafin miliyoyin dala domin jihohin da rikicin Boko Haram ya daidaita.
Yace suna cikin farin ciki da godiya da abun da gwamnatin Amurka tayi. Jihohin Adamawa da Borno da Yobe an basu dalar Amurka fiye da miliyan goma. Tun da jumawa suke kiran kasashen duniya su taimaka musamman jihar Borno, jihar da tafi kowace shan wahalar Boko Haram. Ya kira kungiyoyi da mutanen kirki su tashi su yi hobasa su taimaki kimanin mutane 120,000 da suke sansanin 'yan gudun hijira har yanzu. Akwai kuma kananan hukumomi 22 da suke da 'yan gudun hijira.
Grema ya bada tabbaci taimakon zai kaiga duk wadanda suka kamata su samu saboda mutanen Amurka sun ziyarci jihar, sun kewaya dasu sun kuma zauna dasu sun tattauna. Ban da haka yace ya tabbata Amurka ba zata bayar da makudan kudi haka ba ta kuma juya bayanta. Zata tabbatar an yi abun da take so.Yace zasu yi aiki da gwamnatin tarayya da ta jiha da kungiyoyi domin tabbatar cewa kudin sun kai inda ya kamata.