Wata sananniyracibiyar Elsevier mai buga litattafai da mujalloli a garin charlotte na jihar North Carolina dake Amurka, ta shirya wani taron kimiya inda ta tara masana don yin binciki akan kwayar halitta gado da kuma yadda ake iyi kirkiro wata halitta daga cikinta, wadda zata bada wani abu mai amfani ga amfanin al’umma baki daya. A ta bakin Profesa Fatima Batulu Mukhtar a wata hira da murya Amurka ta yi da ita.
Profesa Fatima Batulu Mukhtar, na daya daga cikin wadanda suka halarci wannan taron. Ta cigaba da cewa, bayan haka su Masu bincike da kirkira zasu fito da abinda don ayi cinikayya akansa yadda alumumma baki daya zata amfana da shi.
Profesa Fatima tace ta yi sha’awar wannan ilimin saboda a cewarta wani sabon bangare ne wanda mutane ke da tantama akansa, ana samun sabanin fahimta da kalubale sosai saboda wannan fanin wani sabon ilimi ne wanda ya kawo canza halittar gadon wata halitta don samun wata halittar da ban. Missali kamar sauya kwayoyin halitar masara wadda bata da jumriyar rashin ruwa da mai jimriyar rashin ruwa.
Kamar yadda zaku saurara a nan ga hirar da muryar Amurka tayi da Profesa Fatima.
Your browser doesn’t support HTML5