Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane da Dama Sun Mutu a Wani Hadarin Mota a Jihar Oyo


Wani mummunan hadarin mota. (File Photo)
Wani mummunan hadarin mota. (File Photo)

Mutane wajen goma da ke sana'a a wani garejin bakin hanya sun gamu da ajalinsu a jihar Oyo, sanadiyyar wani mummunan hadarin mota.

Mutane da dama sun mutu a wani hadarin da ya auku da daren Jumma’a, a gafen titin “Express” da ke kusa da garejin motocin da ke garin Akinyele da ke jihar Oyo, inda aka kai wasu da abin ya rutsa da su asibitin St. Patrick.

Wani ganau mai suna Alhaji Garba Adamu Manu ya shaida ma wakilinmu na Ibadan Hassan Ummaru Tambuwal cewa daya daga cikin motocin ma na dan’uwansa ne mai suna Hamza, y ace wata tirela ce mai shirin hawa kan hanya sai kuma ga wata tilera ta kamfanin Dangote, don haka sai ta koma hannun ‘mai zaman banza’ inda ya tunkuyi wasu kantoci uku, wadanda su ka abka ma masu sana’ar kifi da sauran jama’a.

Wani ganau din kuma y ace mutane wajen goma ne su ka mutu, wadanda su ka sami munanan raunuka ma sun kai kimanin biyar.

XS
SM
MD
LG