Allah Yayi ma Galadiman kano Alhaji Tijjani Hashim rasuwa jiya a jihar kaduna kuma anyi jana’izarsa a kano yau din nan.
Mutane da dama sun bayyana alhinin su game da rasuwar Galadiman, musamman ta la’akari da dabi’arsa, kasancewarsa mutum mai haba-haba da mutane, da sauraron koke-koke da matsalolinsu. Haka kuma Galadiman yayi suna wajen tallafa ma matasa ta samar masu aiki da kuma dafa masu wajen neman na kansu.
Marigayi Alhaji Tijjani Hashim mutum ne mai saukin kai lokacin da yake raye. Akwai abubuwa da dama da bai cika kulawa da su ba, kuma bai kyamaci mutane ba.
Alamomi sun nuna cewa marigayi Galadima jigo ne a fagen siyasa kafin ya rasu, ma’ana da taimakon shi wasu manyan kasar Najeriya suka zama abinda suka zama a yau.
Muryar Amurka tayi hira da wakilinta Mahmud I. Kwari, inda ya bayyana cewa, marigayin ya samo tushen harkokin siyasa ne tun lokacin Majalisar Dokokin arewacin Najeriya, lokacin su Sardaunan Sokoto, inda yayi sakataren majalisar. Ta haka ne ‘yan siyasa da dama suka koyi darussa da dama daga gare shi musamman saboda kasancewarsa na kusa da Sardauna.
‘Yan siyasa da dama sun mutunta shi, sun kuma nemin shawarwari daga gare shi duk da cewa shi Basarake ne ba dan siyasaba a ta bakin Mohammadu I. Kwari.
Kamar yadda za ku ji anan ga hirar muryar Amurka da wakilinta.