Taron kasashe talatin da biyu na shekara-shekara da yanzu a keyi a Jamhuriyar Niger ana yi ne karkashin Hukumar kasuwanci Da Bunkasa Kasa ta Majalisar Dinkin Duniya.
WASHINGTON, DC —
Taron da za'a yi na tsawon kwanaki hudu zai duba dabarorin kyautata huldar kasuwanci kan ma'adanan karkashin kasa har da na man fetur tare da zakulo dalilan da suka sa kasashen da Allah ya albarkacesu da ma'adanan kasa ba sa cin moriyarsu.
Taron ya zo daidai da lokacin da Jamhuriyar Niger ke shirin kawo sauyi cikin kundun tafiyar da arzikin ma'adanan kasarta da kuma niyar sake shawarar kasuwanci da kamfanonin kasashen waje dake hako ma'adanai a cikin kasarta.
Ministan Makamashi da Man Fetur na Jamhuriyar Niger Malam Fumakwai Gado ya ce ribar farko da kasarsa zata ci domin taron shi ne ta saurari duka kasashen duniya da suka riga kasar fara irin wannan aikin. Abu na biyu shi ne sake shirinsu yadda zasu samu riba fiye da yadda suke samu yanzu daga kamfanonin dake shigowa kasar yin kasuwancin ma'adanai. Zasu kaucewa abun dake faruwa yanzu inda kamfanonin waje suka fi kasar samun riba.
Kungiyoyin samar da makamashi ga kowane dan Niger sun yaba da ganin wannan taron domin an jima ana ci da gumin 'yan Niger kan hako ma'adanan kasa inda manya-manyan kamfanonin waje ke wawure anfanin su bar 'yan kasar hannu wofi. Malam Mustpha Kadi jagoran kungiyoyin fararen hula ya ce yana so a ce Niger ta ci rabonta daidai kada a dingi gutsuramata wani dan kaso kawai. Yakamata Niger ce zata yi shugabancin ma'adanan da ta mallaka.
Cikin wadanda suka halarci taron har da Alhaji Ahmed Shehu Yakasai daraktan kamfanonin Dangote wanda ya ce taron yana da mahimmanci domin su da suke sarafa ma'adanan da wadanda ke sayensu duk suna wurin taron. Ya ce wannan wata dama ce suka samu na tattaunawa da juna da kuma fahimtar juna domin kowa ya anfana.
Abdullahi Mamman Ahmadu nada rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5