Taron Gwamnonin Jihohin Arewa Maso Gabashin Najeriya

Gwamnonin jihohin arewa maso gabashin Najeriya - Daga hagu, Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, gwamnan Gombe Inuwa Yahaya da gwamnan Taraba, Agbu Kefas. (Facebook/Jamila J Tanko)

Jihohin yankin na arewa maso gabashin Najeriya, musamman jihar Borno, sun kwashe sama da shekara goma suna fama da matsalar mayakan Boko Haram.

Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya sun gudanar da wani taro don duba kalubalen da ke fuskantar yankin.

Taron wanda ya wakana a birnin Yola na jihar Adamawa, ya samu halartar duka gwamnonin jihohin shida da ke yankin.

Jihohin sun hada da Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da kuma Yobe.

Bayan taron, gwamnonin sun cimma matsayar cewa, duk da matsalar tsaro a yankin na raguwa, akwai bukatar gwamnonin su kara kaimi wajen hadin kai don ci gaban yankin.

Har ila yau, taron ya cimma matsayar cewa akwai bukatar jihohin yankin su karfafa hadin kai da jami’an tsaron kasar don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yaba da irin matakan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake dauka kan batun tsaro a yankin, amma ya ce hadin kan jihohin yankin na da matukar muhimmanci.

Jihohin yankin na arewa maso gabashin Najeriya, musamman jihar Borno, sun kwashe sama da shekara goma suna fama da matsalar mayakan Boko Haram.

Baya ga batun tsaro, taron ya tattauna kan wani shirin kasuwar baje koli da jihar Bauchi za ta karbi bakunci anan gaba.

Kazalika jihar ta Bauchi ce za ta karbi bakuncin taron kungiyar na gaba, wanda za a yi a tsakanin watan Fabrairu da Maris din shekarar 2024.