Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi wata ganawar gaggawa yau Talata dangane da gwajin makami mai linzamin da Iran tayi.
WASHINGTON, DC —
Amurka ce ta bukaci zaman biyo bayan gwajin makami mai linzami mai matsakaicin zango da Iran ta yi shekaranjiya Lahadi. Ba a dai san takamaimai Irin makamin mai linzami ba da kuma irin barnar da zai iya yi.
A shekarar 2015, kwamitin sulhun ya haramtawa Iran gudanar da duk wasu ayyuka da suka danganci makami mai linzami da za a iya yin amfani da su wajen harba makaman nukiliya.
Takunkumin da aka sanyawa Iran na shekaru 8 ya zo ne bayan wata yarjejeniya da Iran da kasashe 6 masu arzikin man petur suka cimma na takaitawa Iran din shirin kera makamai masu linzami don sassaucin takunkumin tattalin arzikin da aka sanyawa kasar.