Da yammacin jiya Litini aka tuhumi Alexandre Bissonnette, dan shekaru 27 da haihuwa, da aikata laifuka 6 na kisan kai da kuma biyar na niyyar aikata kisan kan a harbe-harben bindigar da ya yi,
da Firayim Ministan Canada Justin Trudeau ya bayyana a matsayin "harin ta'addanci kan Musulmi."
Mutane sama da 50 ne suke harabar Cibyar Rayar da Dabi'un Islama, lokacin da harbe-harben su ka auku. Wata mai magana da yawun 'yansanda, Christine Coulombe, ta ce mutane shidan da abin ya rutsa da su 'yan shekaru tsakanin 35 ne zuwa 70. Wasu 8 kuma sun samu raunuka a wannan harin, ciki har da wasu biyar da ke cikin mawuyacin hali.
Da farko 'yan sanda sun kama mutum na biyu a matsayin wani da ake zargi; amma a yanzu ana daukarsa a matsayin shaidan gani da ido.
'Yan sanda dai ba su bayyana dalilin harin ba, kuma har yanzu ba a tabbatar ko akwai hannun wasu kuma a harin ba.
Da ya ke jawabi ga Majalisar Dokokin kasar jiya Litini, Trudeau ya ce an rutsa da mutanen ne kawai saboda irin addinin da su ke bi, sannan ya gaya ma Musulmin da ke Canada, "Mu na tare da ku."