A kuri'un da aka kada 56 akasin 43, Rex Tillerson ya samu goyon baya mai rinjaye a zauren Majalisar da jam'iyyar Republican ke jagoranta da yammacin jiya Litini, kuri'un da su ka zama shimfida ga batun tabbatar masa da mukamin a 'yan kwanaki masu zuwa.
Yawancin 'yan Democrat ba su goyi bayan Tillerson ba, tsohon shugaban kamfanin Exxon Mobil, to amma ba za su iya hana tabbatar masa da mukamin ba, sai ko idan wasu 'yan Republican sun goyi bayansu, wanda wani abu ne mai wuya.
Shugaban marasa rinjaye, dan Democrat Chuck Schumer ya yi kiran da a jinkirta kada kuri'ar tantancewar har sai Tillerson ya amsa tambayoyi kan ikon Shugaban kasa, wanda Trump ya yi amfani da shi wajen bayar da umurnin wucin gadi, na hana shigowar 'yan gudun hijira da matafiya daga wasu kasashe 7 masu rinjayen Musulmi.
Wasu fitattun 'yan jam'iyyar Republican biyu, John McCain da Lindsey Graham, sun caccaki Trump saboda rashin tuntubar muhimman cibiyoyin tarayya kafin ya bayar da umurnin hana shigowar. Sun kuma nuna damuwa kan niyyar Trump ta inganta dangantaka da Rasha. To amma 'yan Majalisar Dattwan biyu ba su nuna alamar za su ja kafa game da tantance Tillerson ba.