Dubban mutane ne dai suka yi ta zanga zanga a wasu biranen kasar kuma ‘yan jam’iyar Democrat sun ce za su dauki wani mataki da zai hana ci gaba da aiwatar da dokar.
A wasu jerin sakonnin Twitter da ya aike da safiyar yau Litinin, Trump ya ce Sakataren Ma’aikatar Tsaron cikin gida ta Homeland Security, John Kelly ya fada mai cewa “komai na tafiya daidai, koda yake an dan fuskanci matsaloli kadan”.
Umurnin da Trump ya sa hanu a ranar Juma’ar da ta gabata, ta hada da dakatar da karbar baki har na tsawon kwanaki 120 da kuma hana ‘yan kasar Iraqi da Iran da Syria da Somalia da Sudan da Libya da Yamal shiga Amurka har na tsawo watannin uku.
“Wannan shirin na tsawon kwanaki 90 ne, domin mu tabbatar da wanda ke shigowa cikin kasarmu. Tsare lafiyar Amurkawa da kasarmu muhimmin abu ne a wurinmu”. In ji Sean Spicer, Sakataren yada labarai a Fadar White House.