Yau Jumma’a bangaren zartaswa na Kungiyar tarayyar Turai zai bullo da wani kuduri na hana kamfanonin kasashen Turai mutunta takunkumin da Amurka ta kakaba ma Iran, a wani mataki na kare yarjajjeniyar nukiliyar Iran da kuma kare harkokin kasuwancin kasashen Turai.
“Wajibi ne mu kare kamfanonin Turai,” a cewar Shugaban Bangaren Zartaswa na kungiyar ta EU Jean-Calude Juncker, bayan wani taron shugabannin kungiyar tarayyar ta Turai jiya Alhamis a Sofia na kasar Bulgaria, “
Ya kara da cewa, “Ya kamata mu dau mataki yanzu, kuma shi ya sa ma mu ka kaddamar da wannan matakin yanzu.”
Juncker ya ce bangaren zartaswar zai fara aiwatar da kudurin hanin, wanda ya hana kanfanonin na EU mutunta takunkumin da kuma zartas da hukunci.
A halin da ake ciki kuma, Shugabar Jamus Angele Merkel ta fadi jiya Alhamis cewa a shirye Kungiyar EU ta ke ta tattauna kan harajin da Shugaban Amurka Donald Trump ya saka kan karafa da dalmar da ake shigo da su Amurka, to amma ta kara da cewa dole ayi bani-gishiri in baka manda.