Jami’an ‘yan sandan jihar sun ce bom ne kirar hannu, kuma yayi sanadiyar jikkata a kalla wasu mata uku.
Daya daga cikinsu wadda ta fi jin rauni yanzu haka tana jinya a asibitin kwararru da ke Jalingo, yayin da sauran biyun kuma aka sallame su daga asibitin nan take.
Kakakin Rudunar 'yan sandan jihar, S.P. Usman Abdullahi, ya shaida wa Muryar Amurka cewa yanzu haka jama'in tsaro sun killace wurin da lamarin ya auku don hana jama'a mu'amalla da wannan yankin.
Wani mai sharhi kan lamarin tsaro a Nijeriya, Kwamred Umar Usman, na ganin ya kamata gwamnatin jihar ta hada kai da jami'an 'yan sanda jihar domin gano inda ake hada wadannan bom na gargajiya.
Ya ce hakan shine zai kawo karshen yawan tashe-tashen wadannan ababen.
Saurari rahoton Lado Salisu Garba a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5