Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Kwastam Sun Yi Sanadin Mutuwar Mutum Hudu a Jihar Adamawa


Jami'an hukumar Kwastam
Jami'an hukumar Kwastam

Lamarin ya auku ne bayan wani hastari da motar hukumar, a lokacin da jami'anta suke bin wani da suke zargi da daukar shinkafa daga kasar Kamaru zuwa Najeriya ba tare da izini ba, a yankin Hayingada da ke karamar hukamar Girei inda mutum hudu suka mutu bakwai kuma suka jikkata.

ADAMAWA, NIGERIA - Yayin tattaunawa da wani abokin daya daga cikin wandanda suka mutu a lokacin hadarin, ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da abin da jami’an kwastam din suka yi har ya yi sanadiyar rasuwar abokin na su.

Wani da ya shaida lamarin da ya bukaci da a sakaya sunansa, ya ce motar kwastim din ta taso ne a guje daga karamar hukamar Girei, suna bin wani mai karamar mota kirar Sitalet wanda har suka shigo yankin na Hayingada inda aka buge mutane da dama, hudu daga cinkinsu suka mutu.

Al’ummar mazauna yankin karamar hukamar Girei sun koka kan yadda ‘yan kwastam din suka dade suna janyo irin wanna hadari, amma hukumar ta yi ko in kula akan alamarin in ji wani dan karamar hukamar Girei da ya bukaci da a sakaya sunansa saboda tsaro.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa SP Sulaiman Yaya Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce yanzu haka tuni jami’ansu suka fara gudanar da binchike a kan al’amarin.

Saurari cikakken rahoto daga Lado Salisu Garba:

 Jami'an Kwastam Sun Yi Sanadin Mutuwar Mutum Hudu a Jihar Adamawa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG