Gwamnatin Najeriya ta fara tantance fannoni daban daban domin gano irin cigaban da aka samu a kasar.
WASHINGTON, DC —
Gwamnatin Najeriya ta fara duba fannonin ilimi, kiwon lafiya, sashen mata da matasa, kananan yara da nakasassu domin tantance irin cigaban da aka samu a wadannan fannoni a duk fadin kasar.
Mai baiwa shugaban kasar Najeriya shawara ta musamman dangane da harkokin inganta rayuwar jama'a Uwargida Sira Hakim ita ce ta furta hakan a Ibadan babban birnin jihar Oyo lokacin da ta ziyarci gwamnan jihar Abiola Ajimobi a ofishinsa. Sassan da ta ambata ta ce suna da mahimmanci kuma idan suka kammala tantancewar zasu fito da wata dabara da zata habbaka ayyukansu kan fannonin. Ta kara da cewa daga karshe zasu yi taro da duk masu ruwa da tsaki a fannonin domin cimma wani tsari da za'a yi anfani da shi nan gaba.
A nashi jawabin gwamna Ajimobi ya ce sun fara ingata jihar yadda kowa da kowa zai yi alfahari da ita. Ya ce suna kokari a wasu fannonin da ta ambata kamar ilimi, kiwon lafiya, sashen mata da yara. Gwamnan ya ce gwamnatinsa zata ba shirin goyon baya.
An zabi jihar Oyo cikin jihohin kudu maso yammacin Nageriya ta zama cibiyar wannan aikin a yankin.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.

Your browser doesn’t support HTML5