Turkiya ta fara gudanar da ayyukan soji da ta dade tana tanadi a arewa maso gabashin Syria domin kawar da rundunar Kurdawa da take mata kallon ‘yan ta’adda, amma kuma kasashen yammacin duniya suka daukarta muhimmiyar kawa wurin yaki da IS.
WASHINGTON DC —
Shugaban Turkiya Racep Tayyip Erdogan ya bada sanarwar fara kai farmakin a yau Laraba, wanda yake kira yunkurin tabbatar da zaman lafiya kana yace manufar aikin sojin ne kawar da barazanar ta’addanci a kan Turikiya.
Ayyukan sojin da Turkiya ta fara, yana zuwa ne ‘yan kwanaki bayan wata sanarwar ba-zata da ya janyowa Washington sukar lamiri, cewa Amurka zata jnye sojojinta daga yankin.
Shugaban Amurka ya fada a wata sanarwa a yau Laraba cewa Amurka ta fito karara ta fadawa Turkiya cewa bata a amince da wannan farmaki ba kuma bai dace ba, sai dai shugaban na Amurka yace babu sojojin Amurka a wurin.