‘Yan jam’iyyar Democrat a majalisar wakilan Amurka sun aika da takardun sammaci ga ofisoshin ma’aikatar tsaron Amurka da na kasafin kudi da ke Fadar White House, a ci gaba da binciken yiwuwar tsige Shugaba Trump da majalisar ta sa a gaba.
Majalisar dai ta nemi ofisoshin da su mika mata takardun da suka shafi shawarar da Trump ya yi na rike tallafin kayayyakin soji da aka warewa kasar Ukraine.
A jiya Litinin, Kwamitoci uku da ‘yan jam’iyyar Democrat ke jagoranta a majalisar, suka bukaci Sakataren Tsaron Amurka, Mark Esper, da mukaddashin Darakta mai kula da kasafin kudi da Gudanarwa da Harkokin Kasuwanci, Russell Vought, da su mika takardun nan da zuwa 15 ga watan nan na Oktoba.
‘Yan jam’iyyar ta Democrat na binciken tursasawar da ake zargin Trump ya yi wa Ukraine na cewa ta binciki abokin hamayyarsa na jam’iyyar Democrat Joe Biden da dan sa, Hunter.
Wani bangare binciken, na so ne ya gano ko matakin da Trump ya dauka na rike tallafin kayayyakin soji da Amurka ta ba Ukraine, na da nasaba ko akasin haka, da bukatar da ya gabatarwa kasar na ta binciki iyalan Biden.
Facebook Forum