Takarar Shugaban Kasa Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Najeriya

Takarar Shugaban Kasa Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Najeriya

Manazarta a fagen siyasar Najeriya da ke sharhi kan harkokin dimokradiyyar kasar, sun fara bayyana mabanbantan ra’ayi dangane da kamun ludayin laffuzan ‘yan takara bayan bude labulen fara kamfe da hukumar zabe ta yi na tunkarar babban zaben 2023.

KANO, NIGERIA - Gudanar da kamfe cikin tsafta ta hanyar kiyaye laffuza, babu kalaman batanci ko cin zarfi a yayin neman kuri’a na cikin muhimman abubuwan dake cikin sabon kundin dokar hukumar zabe ta Najeriya.

Kimanin makonni uku kenan da suka shude hukumar zaben Najeriya INEC ta ba da izinin fara kamfe ga jam’iyyu da ‘yan takarar kuma a Talatar nan ce Jam’iyyar Hamayya ta PDP ta kaddamar da kamfe din ta na shugaban kasa a Jihar Akwa-Ibom, yayin da ita kuma APC mai mulkin kasa ta kaddamar da reshen mata na kwamitin ta da zai tallata ‘dan takarar ta na shugaban kasa, a wani banagre na tunkarar harkokin zaben gadan-gadan.

Takarar Shugaban Kasa Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Najeriya

Dokokin hukumar zabe dai sun haramta kazaman kalamai domin neman kuri’a, kuma tuni ‘yan takarar shugaban kasa na dukkanin Jam’iyyu suka rattaba hannu akan yarjejeniyar tsaftace kalamai yayin kamfe wanda kwamitin dattawan kasa kan lamuran zabe karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Janar Abdussalami Abubakar ya tsara.

Yanzu haka dai masu kula da harkokin siyasa a Najeriya sun fara tsokaci kan kamun ludayin kalaman ‘yan takarar da jam’iyyun su.

Comrade Abdulrazak Alkali shugaban kungiyar OCCEN mai rajin raya tsarin dimokaradiyya a Najeriya, ya ce akwai alamaun cewa, ‘yan siyasar za su yi aiki da wadancan ka’idoji na dokar zabe da kuma martaba yarjejeniyar mutuntaka da suka sanyawa hannu a gaban kwamitin dattawan kasa kan harkokin zabe na tsohon shugaban kasa Janar Abdussalami Abubakar.

Comrade Abdulrazak Alkali shugaban kungiyar OCCEN

Sai dai a ra’ayin Farfesa Kamilu Sani Fagge, Malami a tsangayar kimiyyar siyasa Jami’ar Bayero, Kano, kalaman da suka fito a taron kaddamar da kamfe na Jam’aiyyar PDP a jihar Akwa-Ibom da kuma wadanda suka fita daga zauren kaddamar da reshen mata na kwamitin yakin neman zaben ‘dan takarar shugaban kasa na APC, na nuna da wuya ‘yan siyasar su martaba wadanda can ka’idoji na hukumar zabe da kuma daftarin yarjejeniyar kiyaye lafazi na kwamitin Janar Abdussalami Abubakar.

Fiye da watanni hudu dai za’a kwashe ana gudanar da hada-hadar kamfe din neman kuri’a kana daga bisani a gudanar da zaben shugaban kasa a watan Fabrairun badi.

Saurari cikakken rahoto daga Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Takarar Shugaban Kasa Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Najeriya.mp3