Takaitatcen Tarihin Sakatariyar Gwamnatin Najeriya Dr. Habiba Lawal

Dr. Habiba Lawal sakataren gwamnatin tarayya mai riko

Ta karantu ta kuma yi aikace aikace a fannoni daban daban a mataki jihar da na tarayya

Mai rikon mukamin sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Dr. Habiba Lawal, ‘yar asalin karamar hukumar Toro ne dake jihar Bauchi,

An haifeta a ranar 3, ga watan yuni shekarar 1963, tayi karatun firamare a makarantar firamare na Gyamzo a garin Toro, daga nan sai karatun sakandare wanda tayi a kwalejin gwamnatin tarayya dake Kaduna.

Bayan da ta kammala karatun sakadare sai ta nufi jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, a inda tayi digiri dinta na farko da na biyu, daga bisani kuma ta tafi jami’ar Abubakar Tafawa Balewa inda tayi digirin digirgir.

Har ila yau tayi wani karatun a wata jami’a mai suna Anglia a kasar Biritaniya.

Dr. Habiba Lawal, ta yi koyarwa a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, dake Bauchi, tayi kwamishina, a ma’aikatun ciniki da masana’antu da ma’aikatar al’adu da yawon bude ido a jihar Bauchi, ta kuma rike mukamai daban daban a matakin gwamnatin tarayya.

Dr. Habiba Lawal, ita ke rike da mukamin babbar jami’a a ofishin sakataren gwamnatin tarayya kawo lokacin da aka tabbatar mata da mukamin sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya amma a matsayi na riko.

Your browser doesn’t support HTML5

Takaitatcen Tarihin Sakatariyar Gwamnatin Najeriya Dr. Habiba Lawal - 4'16"