Da yake bayyana alfaharinsa a cikin wannan mako, Trump ya ce babu wata gwamnati da ta samu nasarori tsakanin 90 kamar yanda shi ya samu a wurin inganta harkokin soji da iyakokin kasar da cinikaiya da jami’an tsaro, yace muna kaunar jami’an tsaronmu da kuma rawa da gwamnatinsa ta taka wurin kyautata harkokin gwamnati.
Da yake yabawa kansa, Trump ya ambato harin makami mai linzami da Amurka ta kai a Syria a makwanni biyu da suka wuce a matsayin martani na makamai masu guba da gwamnatin kasar ta yi amfani da su a kan fararen hula a matsayin wani babban nasara.
A ra’ayoyin Amurkawa da aka tattara, kashi 52 cikin dari da basu ra’ayin yanda yake gudanar da gwamnatinsa; sun rinjayi kashi 42 cikin dari na masu ra’ayinsa.
Facebook Forum