A kwanan nan dai wata ciubiyar mai nazari akan tattalin arziki na duniya da ake kira “World Economy” dake da hedkwatar a London, tayi bayanin cewa Najeriya ta fita daga kangin tattalin arzikin da take fama dashi a ‘yan shekarun nan.
A rahoton wannan cibiya dake da hedkwatar a birnin London ta fitar tace an samu karuwar saye da sayarwa a hada hadar kasuwanci ta Najeriya, masamman ma dai a watan Maris da ya kabata inda hada hadar ya kai na kasha hamsin da uku da digo biyar ( 53.5%) cikin dari abinda dake zama mafi girma a ‘yan shekarun nan. Wannan ya nuna alamun cewa farashin kayayyaki yau da kullum sun sauko.
Dr. Isa Imam, wani Malami a sashen koyar da nazarin tattalin arziki a jami’ar kimiya da fasaha dake Minna, yace idan dai ana maganar “Recession” watau koma baya na tattalin arzikin kasawani hali ne da kasa kan sami kanta a ciki na cuncin rayuwa da hauhawar kayayyaki da rashin aikin yi da kuma gurguncewar masana’antu.
Sai kuma duk da wannan rahoto da wannan cibiyar ta fitar ‘yan Najeriya, sunce har yanzu basu gani a kasa ba wata mata mai suna Judith, ta shedawa wakilin muryar Amurka Babbngida Jibrin, cewa kayayyaki sunyi tsada hatta pure water tunda ya tashi bai sauko ba muna kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya yi kokari yayi wani abun wajen ganin kayayyaki masarufi sun sauko.
Facebook Forum