Yanzu haka an soma samun takun saka a tsakanin gwamnatin jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya da kungiyar tsoffin ma’aikatan jihar wato yan fansho,musamman tsoffin manyan sakatarorin wato permanent secretaries bisa batun rashin biyansu hakkokinsu na sallama.
Tada jijiyar wuyan kuwa ya biyo bayan da jihar ta karbi kudadenta daga kason Faris kulob na sama da Naira biliyan tara da gwamnatin tarayya ta bada ga jihohi.
Kungiyar ta tsoffin manyan sakatarori watau “Permanent Secretary” wanda ya hada da akawun majalisar dokokin jihar da kuma tsoffin alkalai na kokawa da rashin kula da gwamnatin jihar ke nunawa da halin da suke ciki a yanzu na rashin samun hakkokinsu tun bayan barin aiki.
Shugaban kungiyar manyan sakatarorin Mustapha Galadima, yace basu amfana da ko kwabo ba da tallafin da gwamnatin tarayya ta rabawa jihohi da mana Faris kulob ya bayana hakka ne a wani taron manema labarai a Yola fadar jihar Adamawa.
Ya kara da cewa abin takaici shine ikirarin da gwamnatin jihar tayi na ware wani kaso daga kudin Faris kulob, domin biyan kudaden salaman su.
Kwamishinan yada labarai na jihar Ahmed Sajo, yace dokokin gwamanati daban daban suke yana mai cewa akwai manyan sakatarori wadanda suka yi ritaya a lokacin da mikamin babban sakatare watau “Permanent Secretary” baya cikin wannan sabon tsari na yanzu. A lokacin da su kayi ritaya sun yi haka ne akan dokoki na wance lokacin akwai kuma manyan sakatarori watau “Permanent Secretary” wadanda sukayi ritaya a yanzu wanda doka tace a biyasu albashin da ake biyansu kafin suyi ritaya har na tsawon rayuwarsu, su kuwa basu cikin wannan tsari amma suka ce suma sai a sasu a cikin wannan sabon tsari inda aka sami takaddama Kenan.
Facebook Forum