Takaita Zirga Zirgar Ababen Hawa a Maiduguri

Gwamna Kashim Shettima

Gwamnatin jihar Borno, ta takaita zirga zirgar ababen hawa daga ranar Jumma’a zuwa ranar Lahadi.

Gwamnatin dai tace ta dauki wanna matakin ne bisa dalilan tsaro ganin irin yadda akan kai hare haren Boma Bomai akan jama’a.

Wannan sanarwa dai mai dauke da sa hannun sakataren Gwamnatin jihar ta Borno, Alhaji Njidda Shuwa, yace za’a takaitazirga zirgar ababen hawa ne har zuwa ranar Lahadin dan ganin cewa an kare lafiya da dukiyoyin jama’a.

Shekaru ukku, kennen ana daukar irin wannan mataki a duk lokacin bukukuwar Sallah ko na Kirisimiti, bisa mataikan tsaro da hukumomin tsaron kasar ke dauka.