Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kere-Kere Baiwa Daga Allah, ga Kowane Matashi


Kere-Kere abubuwan more rayuwa
Kere-Kere abubuwan more rayuwa

A rayuwa kowane mutun da Allah, ya hallita yayishi da irintashi basirar, wani matashi Sale Musa, yayi karin bayani dangane da yadda yake amfani da irin tashi basirar da Allah, yayimasa. Yakan kera motoci, jirage, gidaje, da dai makamantansu.

Allah, yasa mishi son kere-kere tun yana yaro, wanda a yanzu yakan yi amfani da irin basirarshi ya keri abubuwa, domin bayynar da irin tashi basirar ga matasa ‘yan’uwanshi. Wanda tahaka yake kokarin jawo hankalinsu matasa da suma suyi kokarin ganin sun nunarda irin tasu basirar, da fatan nan gaba su samar da masu yin a gaske a rayuwa.

Kuma burnish da na matasa irinshi shine idan Allah, yasa gwamnatoci da masu hannu da shuni zasu taimaka, akwai bukatar suje makarantun kere kre donmin inganta basirarsu, amma wannan wani abune da ke bukatar kudi, wanda basu da wanna zarafin. Amma fatansu shine Allah, yasa wani ya dubesu domin mika sunansu ga hukumomi. Yana da bukatar yaje makarantar kere kere domin yana da yakinin cewar zai iya gina mota ta gaske idan yasamu taimako daga kwararru.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG