Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Wawure Filin Makaranta Yana Kokarin Tafka Makeken Gini


Wata takaddama ta barke a tsakanin shuwagabanin wata makarantar Firamari dake Minna ta jihar Neja, da tsohon shugaban ma’aikatan jihar ta Neja, Barrister Abbas Bello.

Shugabanin wannan makaranta dai mai suna {Waziri Primary School} sun koka ne akan yadda suka ce tsohon shugaban ma’aikatan Barrister Abbas Bello, ya wawure filin makarantar yake kokarin tafka wani makeken gini a filin.

Shugaban makarantar Muhammad Abdullahi, yace” yatare gaban makaranta wanda yasa makarantar a sako, wannan ginin tun shekarar 2005, ake jayayya akansa, duk wanda ya duba yasan cewa wannan fili na makaranta ne na ‘yayan talakawa da ake basu ilimi a wannan wuri.”

Suma dai iyayen yara a makarantar ta Waziri, da ta share sama da shekaru saba’in a duniya, sun ce lamarin na matukar cimasu tuwo a kwarya.

A halin yanzu dai kungiyar Malaman makarantu a jihar Neja, tace tana sane da wannan matsala kuma tuni ta fara daukar mataki inji shugaban kungiyar Malaman Ibrahim Umar Bida .

Tsohon shugaban ma’aikatan na jihar Neja, Barrister Abbas Bello, yace” shuwagabanin makarantar basu da hujja, kuma duk wani wanda yayi korafi akan wannan Magana toh lalle baida cikakken sani akan abunda ya faru, a matsayi na na tsohon shugaban ma’aikata babu yadda za’a yi in shiga filin m,akaranta, ina da sani cewa kafin in soma gini a wannan wurin akwai gine gine da aka yi duk filayen nan filayen makaranta ne mai suka yi akan wannan kafin Magana na.”

XS
SM
MD
LG