Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faranta ma Maraya Rai Babbar Ibada ce


Yara marayu
Yara marayu

Marayu bayin Allah, daya daga cikin koyarwar wannan watan Ramadana mai albarka shine, taimaka ma marayu. Kungiyar mai tallafawa mata ta FOMWAN, reshen karamar hukumar Fagge, sunyi wani abun yabawa. Mambobin wannan kungiyar sunyi amfani da wannan lokaci domin taimakama marayu, inda suka sayama yara marayu kayan sallah.

Mafi akasarin ayyukan lada da akeso mutun yayi a cikin wannan watan, shine ya farantama wani ransa, sun kuwa yi kokarin ganin sun sa wadannan yaran cikin farinciki, domin kuwa wadannan yaran sun bayyanar da farincikinsu da samun wadannan kayan sallar, domin suma suyi dai daito da sauran yara.

Hajiya Habiba Aliyu, shugabar kungiyar ta karamar hukumar Fagge, ta bayyanar da wannan a matsayin wani abu da yakamata ace masu hannu da shuni, susa kansu cikin irin wannan ayyukan alkhairi, kuma makasudin yinhaka shine domin kuwa suna da masaniyar ba kowa ke maida hankali wajen gani ya tallafawa irin wadannan mabukatan ba. Don haka suna kira da babbar murya da mutane suji tsoron Allah, su kokarta wajen ziyartar gidajen marayu domin ganin halin da suke ciki, domin kuwa suna neman taimakon al’umah.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG