Wannan na zuwa ne lokacin jigajigan jam'iyar APC mai mulkin kasar ke rasa ‘ya'yanta wadanda ke komawa PDP a Jihohin Kebbi da Sokoto dake arewa maso yammacin Najeriya.
Bayan kammala zabubukan tsayar da ‘yan takara na jam'iyun siyasa a Najeriya, jam'iyun sun fara daura damara ta ganin yadda za su samu galaba a manyan zabukan da za su gudana a shekara ta 2023.
Sai dai kuma wasu jam'iyyun suna fuskantar barazana ta ficewar wasu jigogi zuwa wasu jam'iyu, kamar yadda yake faruwa a jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya inda Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya Sanata Muhammad Adamu Aliero da mai wakiltar Kebbi ta Arewa Sanata Yahaya Abdullahi suka fice tare da magoya bayansu zuwa jam'iyar adawa ta PDP.
Wannan takaddama tsakanin bangaren Adamu Aliero da na gwamna mai mulki yanzu Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ta jima kuma uwar jam'iyar ta kasa warware ta, abin da ya kara tunzura bangaren na Aliero.
A nata bangaren jam'iyar dake mulki a Najeriya da ma jihar Kebbi ta APC ta ce ba ta da masaniya akan fitar Sanata Aliero da mutanensa, a cewar kakakinta Isa Assalafi.
Ku Duba Wannan Ma 2023: NNPP Ta Tsayar Da Kwankwaso A Matsayin Dan TakarartaSu kuwa ‘ya'yan jam'iyar ta PDP cewa suka yi sukan sun yi tsintuwar dame a kala, a cewar mataimakin shugaban jam'iyar PDP mai kula da Kebbi ta tsakiya Haruna Haruna Mai Jega.
Yanzu dai Jam'iyar ta PDP ta baiwa Sanata Adamu Aliero da Yahaya Abdullahi takarar kujerin Sanata na Kebbi ta tsakiya da Kebbi ta arewa, kuma abin da zai dauki hankalin jama'a shi ne, yadda za'a fafata ga neman kujerar sanata na tsakiya tsakanin gwamna mai ci yanzu wanda APC ta tsayar da kuma tsohon gwamna wanda PDP ta tsayar.
A jihar Sokoto ma an kammala dukkan shirye-shirye na karbar wasu jigajigan jam'iyar APC zuwa PDP wadanda suka hada da ‘yan majalisar dokokin jihar da na tarayya duk da yake ba'a ayyana ranar da za'a karbe su ba.
Dama masana kimiyar siyasa sun bayyana cewa sauyin jam'iya dama ce ta dan siyasa amma ana yinta ne a Najeriya idan dan siyasa ya hango akwai matsala ga jam'iyar da yake abinda suka ce yana da illa ga dimokradiya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5