Wasu daga cikin 'yantakara ne dai suka bukaci masu zaben yantakatar na PDP da su yi amfani da katin zabe ko national ID card ko kuma E-pasport domin kada kuri’ar su.
Tsohon Ministan wajen Nigeria, Alh. Abubakar Tanko yace basu taba gani irin wannan tsari ba.
Lawyan PDP a jihohin Arewa ta tsakiyar Nigeria Barista Isyaku Barau yace tsarin bai sabawa kundun tsarin Mulkin PDP ba.
Shugaban PDP na jihar Neja, Barista Tanko Beja yace za a gudanar da zaben a ranar Alhamis din nan.
Mataimakin Gwamnan Bayalsa Laurance Obarawharienwo da PDP ta turo jihar Nejan, ya tabbatarwa manema labarai cewa, zasu warware duk wasu matsalolin da su ka yi tarnaki a zaben.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: