Takaddama Kan Gonaki Tsakanin Jami’ar Bayero Da Wasu Al’umomin Jihar Kano

Bayan fiye da shekaru 30 da gwamnatin jihar Kano ta mallaka gonakan wasu al’umomin kimanin kauyuka bakwai ga jami’ar Bayero, yanzu haka wasu daga cikin al’umomin na ikirarin diyyar gonakai daga mahukuntan Jami’ar.

A tsakanin shekarun 1970 zuwa 1982 ne akayi aikin biyan diyyar gonaki da gidajen al’umomin kauyukan Rimin Gata da Langel da Rijiyar Zaki da Kududdufawa da Dausayi da Katsinawa da kuma Ciromawa bayan da gwamnatin jihar Kano ta wancan lokaci da mallakawa mahukuntan Jami’ar Bayero wadannan wurare, a wani mataki na samar da sabon matsugunni ga Jami’ar.

Sai dai a ‘yan shekarunnan, wasu daga cikin ‘yaya da jikokin mutanen kauyukan na korafin cewa, gwamnati ba ta biya iyayen su diyya ba, gabannin a mallake musu gonaki, don haka suke Muradin lallai mahukunatan Jami’ar ta Bayero su biyan su hakkin su.

Farfesa Adamu Tanko, maitaimakin shugaban Jami’ar Bayero mai kula da harkokin gudanarwa, ya ce a dalilin wannan korafe-korafen da ake yasa jami’ar ta kafa wani kwamiti da binciki lamarin, kuma shine ke shugabantar kwamitin.

Ya ci gaba da cewa rashin tashin mutanen da aka biya diyya a wancan lokacin daga gidajensu da gonakinsu, shine ya yi sanadiyar wannan magana ta sake tasowa.

Duk da cewa, wadancan al’umomi ba su tunkari majalisar karamar hukumar Ungogo ba, wadda wadanda yankunan ke karkashin ikon ta, amma karamar hukumar na goyon bayan yunkurin muddin akwai hujja, inji Kansilan mazabar Rijiyar Zaki Hon Rufa’I Mohammed Rimin Gata, wanda ke wakilatar shugaban karamar hukumar a cikin kwamitin

Jarman Kano Farfesa Isa Hashim wanda ke wakiltar masarautar Kano a kunshin kwamitin, ya ce masarauta da jami’a duk na jama’a ne, saboda haka duk wani da yake ganin an kware shi ya gabatar da dalilinsa domin a dauki mataki.

Sai dai suk da haka, mahukuntan Jami’ar ta Bayero sunce bayan karkare wannan batu zasu ci gaba da bada aron gona ga duk magidancin dake muradi gabanin aikin fadada jami’a ya isa yankin.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Rikici Kan Gonaki Tsakanin Jami’ar Bayero Da Wasu Al’umomin Jihar Kano - 3'34"